Miji ya fashe da kukan farin ciki bayan matar sa ta biya masa bashin N1.3m


Wasu gajerun bidiyo guda biyu na nuna martanin wani mutum dan Najeriya bayan matar sa ta biya masa bashin miliyan 1.3 da ake binsa, Labarunhausa ta ruwaito.
Matar ta ce, mutumin ya dau tsawon shekaru yana biyan bashin da ake binsa duk wata, amma duk da haka bai gama biya ba.
Yayin da matar ta kira shi cikin dakin su don ta shaida masa ta biya sauran bashin da ake bin shi da kudin da take tara wa, fashe wa da kuka yayi don farinciki.
Bidiyon wata mata yayi yawo a kafafan sada zumuntar zamani, lokacin da mata ta shaida wa mijinta ta biya masa bashin da ake bin shi.
Ta ce bata biya mishi bashin don ta nuna tana da kudi ba, sai don hankalin shi ya kwanta.
Matar ta bayyana yadda mijin ya aro kudi daga banki shekaru uku da suka wuce, saboda ya dauki nauyin iyalin sa.
A cewar matar, mutumin ya dau lokaci yana biyan kudin duk karshen wata. A lokacin da matar ta tare wurin shi a kasar waje, a zaton ta zata samu aiki ba da jimawa ba.
Ta kara da cewa, ta dade tana fatan Ubangiji ya hore mata yadda zata biya mishi bashin.
Ta bakin nata: “Na dade ina tari saboda inaso inga mijina a farinciki. Inaso inga hankalin shi ya kwanta daga fadi tashin da yake.”
Bayan ta samu cikkaken bayani game da yawan kudin da ake bin mijinta, ta gane cewa akwai sauran N1,372,624.69 da ya kamata ta biya. Sai kawai matar ta biya duka.
View this post on Instagram
View this post on Instagram
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






