Labarai

Matasa sun nemi wata makaranta ta hana sanya hijabi a India

Matasa sun nemi wata makaranta ta hana sanya hijabi a IndiaRikici kan hana ɗalibai mata sanya hijabi a’a kudancin Indiya ya tsallaka zuwa Uttar Pradesh, inda wani gungun matasa su ka nemi wata makaranta da ta hana sanya hijabi.
A makon da ya gabata ne dai mahukunta su ka kulle makarantu a Karnataka da ke kudancin India bayan da sabuwar dokar sanya kayan makaranta ta hana ɗalibai sanya ɗan-kwali a cikin aji, lamarin da ya haifar da bore da ga ɗalibai Musulmai, inda su kuma ɗalibai ƴan addinin Hindu su ka yi zanga-zanga ta maida martani.
Daily Nigerian ta ruwaito musulmai, waɗanda yawan su kashi 13 ne a kan yawan yan addinin Hindu da ya kai biliyan 1.3 na al’ummar ƙasar India, sun yi korafin cewa a na gallaza musu da nuna musu bambanci.
A Uttar Pradesh da ke arewacin India, kuma boda da New Delhi, wani gungun matasa sama da dozin biyu sun je makarantar Dharma Samaj College a lardin Aligarh a ranar Litinin, inda su ka mika takardar yarjejeniya kan cewa a hana sanya hijabi kwata-kwata.
Shigaban makarantar, Mukesh Bharadwaj ya ce sun saba su na sanya ƙyalle a wuyan su irin wanda Hindu su ke saka wa, inda ya ƙara da cewa shi bai gane mutanen ba.
A halin yanzu an hana sanya riguna na addini a ajujuwa, sai dai a wani gurin daban.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA