Aljeriya za ta fara biyan matasa marasa aikin yi har sai sun samu aiki
Jaridar bbchausa ta su ruwaito cewa shugaban kasar aljeriya yayi alkawalin baiwa matasa marar aikin yi tallafin duk wata har sai sun samu aiki.
“Shugaban Aljeriya ya ce zai ɓullo da tsarin biyan matasan da ba su da aikin yi a ƙasar yayin da take fama da adadin marasa aikin.
Shugaba Abdelmadjid Tebboune ya faɗa wa ‘yan jarida cewa za a fara biyan matasan ‘yan shekara 19 zuwa 40 daga watan Maris.
Waɗanda suka cancanci shiga tsarin za su karɓi kuɗin da ya kai kusan dala 100 duk wata, da kuma wasu tallafi na lafiya, har sai sun samu aikin yi.
Da yake ba da sanarwar, Mista Tebboune ya ce Aljeriya ce ƙasa ta farko da ta fito da irin wannan shiri wadda ba ta Turai ba.
Ya ƙara da cewa akwai marasa aikin yi 600,000 a ƙasar.”