LabaraiOpportunity

Yadda Zaka Dawo da Email da Password dinka na Npower idan ka Manta

Kamar de yadda Kuka sani Npower wani Shiri ne na daukar matasa miliyan 1 wanda ya fara da daukar masu cin gajiyar 510,000 a watan Agustan 2021 a matsayin Npower Batch C stream1, A halin yanzu shirin zai sake daukar sauran masu amfana 490,000 a matsayin Npower Batch Stream II.

Sai de kuma wasu daga cikin wanda suka cike wannan shirin na Npower sun manta email da password dinsu, wanda sai da shi za a samu damar shiga Shafin Npower domin ka duba matsayinka.

Idan kana daya daga cikin wanda suka manta Login nasu wati Email da password, karka damu yanzu zaka dawo da abunka cikin sauki Insha Allah

Yadda zakayi ka dawo da login din naka shine: ka shiga shafin https://nasims.gov.ng idan ya bude saika shiga wajen Forgot Password saika shiga ka zabi email dinka saika sanya email din naka sannan ka danna Reset password, bayan ka danna daga nan zasu tura maka sako ta email din naka wanda yake dauke da wani Link wanda zaka danna ka chanja password dinka.

Saika danna saika chanja, shikkenan ka chanja password din naka daga nan sai kazo kayi Login shikkenan…

Idan kuma ka gwada waccan hanyar bai yiba saika kira wannan number: 018888148 bayan ka kira saika jira har sai sun daga daga nan sai kayi musu bayani akan matsalar ka, wato ka manta password da email dinka wanda zakayi login na shafin Npower, daga nan su kuma zasu duba sannan su baka damar yin Reset na email da password din.

Allah ya taimaka.

Sources: Hikimatv

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button