Labarai

Majalisar Dokokin Zamfara ta tabbatar da Hassan Nasiha a matsayin sabon Mataimakin Gwamna

Majalisar Dokokin Zamfara ta tabbatar da Hassan Nasiha a matsayin sabon Mataimakin Gwamna Awanni kaɗan bayan tsige Mahdi Aliyu Gusau, Majalisar Dokoki ta Jihar Zamfara ta tantance Sanata Hassan Nasiha a matsayin sabon Mataimakin Gwamna.
Nasiha shine Sanata mai ci da ke wakailtar Zamfara ta tsakiya a Majalisar Dattijai.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa Ƴan majalisar sun tabbatar da Nasiha a matsayin sabon Mataimakin Gwamna a wata ƙuri’a ta bai-ɗaya.
Gwamnan Jihar, Bello Matawalle, a wata wasiƙa danya rubuta wa Sakataren Gwamnati, Kabiru Balarabe sannan Kakakin Majalisar, Nasiru Magarya ya karanta a zaman majalisar na yau Laraba, ya miƙa sunan Nasiha a matsayin sabon Mataimakin Gwamna bayan cire Mahdi Aliyu.
Sai Shugaban Masu Rinjaye, Faruku Dosara ya miƙa ƙudurin tabbatar da Nasiha, wanda dukka mambobin su ka amince.
Kakakin Majalisar ya baiyana cewa naɗin sabon Mataimakin Gwamnan ya yi daidai da tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa na 1999.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button