LabaraiUncategorized
Yansanda a Jihar Kaduna sun ceto wani yaro dan shekara biyar da wata mata ta sato daga Kano.
Advertisment
‘Yansandan sun dakile yunkurin matar na guduwa da yaron zuwa wani gari da ba su bayyana ba.
Sunan yaron Abdulkarim Sani. Ana neman iyayensa ko ‘yan’uwansa da su garzaya wajen hukamar ‘yansanda ta Jihar Kaduna don karbarsa.
Shafin jaridar Daily Nigerian su wallafa wannan bidiyon ga shi nan sai ku saurara kuji.