Labarai

“Ina fama da hawan jini da ciwon siga”, in ji Abba Kyari yayin da ya ke ɗaure a hannun NDLEA

"Ina fama da hawan jini da ciwon siga", in ji Abba Kyari yayin da ya ke ɗaure a hannun NDLEAMataimakin Kwamishinan Ƴan Sanda, DCP, Abba Kyari ya koka cewa ya na fama da rashin lafiya tun sanda Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, NDLEA ta damƙe shi.
A makon da ya gabata ne dai Ƴan Sanda su ka kama Abba Kyari su ka kuma miƙa shi ga hannun NDLEA bisa zargin safarar hodar ibilis.
Daily Nigerian sun ruwaito cewa da ga nan ne sai Kyari, wanda tuni Hukumar Aikin Ƴan Sanda ta dakatar da shi, ya kai Gwamnatin Taraiya ƙara a bisa ci gaba da a ke da tsare shi a NDLEA.
A ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22, Kyari ya roƙi kotu da ta bada umarnin a bada shi beli.
Karin ya nemi kotu ta yanke hukunci na wucin-gadi a kan cewa ya na fama da hawan jini da ciwon siga, sabo da haka ya na buƙatar a bashi kulawa ta gaggawa.
Sai dai kuma Mai Shari’a Inyang Ekwo ya ƙi biyan wannan buƙatar ta Kyari a kan hujjar cewa akwai wasu bayanai a cikin ƙunshin roƙon na sa da su ke buƙatar a ji ta bakin gwamnati.
Ekwo ya ƙara da cewa duk wasu bayanan shari’ar a miƙa su ga gwamnatin taraiya, inda ya saka ranar 24 ga watan Febrairu domin dukka ɓangarori biyun su gurfana a gaban sa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

5 Comments

  1. I pray for God to save a truthful and innocent person,and we as Nigeria we should continue with blessing and praying our country. finally we pray for God to give us qualitative and productive leader in all level of tree arm of government.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button