Labarai

Gwamnan Sokoto ya Kai kudrin Gyaran doka ga Majalisar jihar domin Ragewa Sarkin Musulmi Karfi da Iko

Gwamna Ahmed na Sokoto ya samu amincewar majalisar zartaswar jihar domin mika wani kudiri ga majalisar dokokin jihar da ke neman yin gyara ga dokar da ake da ita na nadi da tsige sarakunan gargajiya a jihar Sokoto. Za a gabatar da kudrin don yin tambari a ranar Litinin

Mafi yawa, kudirin na neman a kwacewa sarkin musulmi gaba daya ikon nadawa, dakatarwa, hukuntashi, mika mulki da dai sauransu, duk wani basaraken gargajiya har zuwa mai unguwa.

Majiyarmu ta mikiya ta ruwaito mana cewa, Iko daya zai kasance waje daya, kuma ya kasance ga gwamna gaba daya ba tare da tuntubar kowa ba.

Ga bidiyon nan ku saurara.

 

 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button