Na sadaukar da duk kudin da fim din NADEEYA ya kawo a cinema ga marasa karfi – Rahama sadau
A shirin da Jaruma Rahama Sadau tayi da Main Hun Khan cikin shirin LARKI LARKA a tashar Liberty Radio 103.3 FM Kano jarumar ta sadaukar da dukkannin kudin da sabon film dinta NADEEYA ya kawo a Cinema ????️ cikin gidauniyar tallafawa marasa karfi ta RAY OF HOPE. Allah ya saka mata da alheri.
Main Hun Khan wanda ya gabatar da shirin yayi rubutu inda ya tabbatar da cewa rahama sadau tayi wannan alkawali na taimawaka marasa karfi da duk kudin da shirina nadeeya ya kawo a cinema wanda haryanzu ana kallonsa a cinema.
“Masha Allahu a hirar da nayi da rahama sadau yau wanda ta sadaukar da abinda ta samu na film dinta da ake haskawa acikin kwana kenan ga marayu da gajiyayyu”
A tattaunawar da akeyi yanzu kai tsaye da Jaruma @Rahma_sadau a @LibertyTVNews ta sanar da cewar ta sadaukar da duk cinikin da film din #NadeeyaTheMovie yayi ga gidauniyar ta tallafawa marasa karfi @RayOfHopeN.
Wannan mahimmin abu ne da ya cancanci jinjina. pic.twitter.com/c2B3wyfzQf— Labaran Kannywood (@Hausafilmsnews) February 20, 2022
Advertisment
Tabbas wannan abun yayi matukar sha’awa duba da irin yadda ta dauki wannan alkawalin taimawaka gajiyayu da kuma marayu.
Allah ya da da budi
Yiwa kaine,Allah saka mata da abinda tayi niyya.