Labarai

Kotu ta jaddada dokar da ta ce duk ƴar sandan da ta yi cikin shege a kore ta

Kotu ta jaddada dokar da ta ce duk ƴar sandan da ta yi cikin shege a kore ta
Wata Babbar Kotun Taraiya a Abuja, a yau Litinin, ta kori ƙarar da Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa, NBA ta shigar gabanta, kan cewa ta haramta wasu sharuɗɗa na Dokokin Rundunar Ƴan Sandan Nijeriya, NPR.

Kamar yadda majiyarmu ta samu daga jaridar Daily Nigerian tana cewa da ya ke yanke hukunci, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya baiyana cewa babu wani laifi a kan sharuɗɗan na 126 da 127 na Dokokin Rundunar Ƴan Sandan Nijeriya, NPR ɗin.

A cewar Mai Shari’a Ekwo, tunda dai an ɗauke ta aiki a Rundunar Ƴan Sanda, sannan ta na sane da waɗannan dokokin, to laifi ne ga ƴar sanda ta karya waɗannan dokokin.

Ita NBA ta na muhawarar cewa sharuɗɗan 126 da 127 na NPR da a ka kafa su kan ƙadamin dokar da ta kafa Rundunar Ƴan Sanda, sun ci karo da sashi na 37 da 42 na Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa.

Kanfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa sharaɗi na 126 ya tanadi cewa, a na baiwa ƴar sanda mai aure, wacce ta samu ciki, hutun haihuwa, kamar yadda doka ta tanada.

Haka-zalika, sharaɗi na 127, ya tanadi cewa, idan ƴar sanda maras aure ta yi ciki to za a kore ta da ga Rundunar Ƴan Sanda ta Ƙasa, kuma ba za a sake ɗaukar ta aikim ɗan sanda ba sai dai da yardar Sifeto-Janar na Ƴan Sanda.

A hannu guda kuma, sashi na 37 na Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa ya baiwa ƴan ƙasa ƴancin yin rayuwar aure ko zaman kai.
Shi kuma sashi na 42 ya bada cikakken ƴancin ɗan adam da ka hani ga a nuna masa bambanci.

NBA ta kuma nuna cewa sharuɗɗan na NPR, ba ma wai sun nuna bambanci ga ƴan sanda mata marasa aure ba, ya sanya da yawa da ga cikin su ba su da ƴaƴa sabo da tsoron kora.
– Daily Nigerian

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button