Labarai
An kama matashin daya yanke kan yaro da kwakule masa idanu a Bauchi (hotuna)
Advertisment
Yansanda a jihar Bauchi sun kama wani Musa Hamza dan shekaru 22 da zargin yanke ka8 da kuma kwakule idanun wani yaro dan shekaru 17, Adamu Ibrahim.
Kakakin ‘yansandan jihar, DSP Ahmed Muhammad Wakili ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an kama wanda ake zargine unguwar Wake dake Alkaleri na jihar, ranar 21 ga watan Disamba.
Yace Musa ya ja Adamu zuwa daji wanda kuma makwabcinsu ne inda ya kasheshi ya kwakule idanunsa.
Kamar yadda Hutudole na ruwaito.Ya binne gawarsa a dajin, amma bayan da aka kamashi ya kai jami’an tsaro inda yayi aika-aikar sannan yace wani Boka ne ya sanyashi ya kawo idanun mutum dan ya masa Tsafin da zai yi kudi.