AddiniLabarai

Sabon Tonon Asiri : Dalilin da yasa ankayi sulhu da Turji da Kisan Mutanen Anka da Bukuyum – Murtala Assada

Advertisment

Mai Girma Shugaban qasa! Gwamnonin Sokoto Zamfara kuji tsoron Allah!! kusani qyale wannan Ta’addanci yana’ci gaba da yad’uwa cikin al’umma, Ba komi bane face fito na fito da Shari’ar Musulunci. Haqiqa Zaku zama Abin tambaya a ranar qiyama. Tunda Annabi (S.a.w) ya ce: “Dukkaninku makiyaya ne, kuma kowanenku Za’a tambayeshi akan Abinda Anka Bashi kiwo”.
Munsan akwai ‘Dai-‘Daikun Malamai dake Qoqarin fadakar da al’umma har Daku illar wannan Ta’addanci. Duk da yake Hausawa na cewa, Dambu idan yayi yawa Bayajin mai! To amma akwai hanyoyin Da zakubi domin warware wannan matsalar in da gaske kukeyi. Kada wannan matsala don kunyi Sakaci ta girma, tafi qarfinku. Kenan Ina amfanin Hukuma? Tunda ita hukuma An kafa’tane kawai, domin ta kare Muradun Talakawa.
Rashin damuwarku da Rayukkan dake Salwanta a Sokoto da Zamfara Ya Sabama tsarin mutunta ‘yancin ‘Dan Adam. Ya ci karo da qa’idar Shugabanci na Adalci da Hankali da Lafiyayyen tunani. Sannan Ya Sabama duk wata Doka ta ‘Dan Adam, Ballantana Dokar Allah Wadda ta Safko daga Sama.
Saurari cikkaken bayyani daga murtala Assada.
https://youtu.be/_6RaFGh0R6U

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button