Kannywood

Shin Da Gaske Sarkin Waka Nazir M Ahmad ya Mutu ?

Advertisment

Shin Da Gaske Sarkin Waka Nazir M Ahmad ya Mutu ?Fitaccen mawakin nan na Hausa, Naziru M. Ahmad wanda aka fi sani da Naziru Sarkin Waka ya musanta labarin da ake yaɗawa a shafukan sadarwa na zamani akan cewa wai ya rasu sakamakon wani mummunan hatsarin mota.
Naziru Sarkin Waƙa ya bayyana hakan a yau Litinin a shafinsa na Facebook, inda dubban mabiyansa su ka yi masa fatan alkhairi tare da ƙaruwar arziki.
“To saurin me kuke ne?? Allah ya shirya ku mukuma ya kyautata karshenmu amin”. In ji Naziru.
Tun da farko dai shafukan sadarwa na zamani sun cika da labarin rasuwar Naziru Sarkin Waƙa. Wanda kuma zancen ba shi da tushe balle makama.
Wani bincike da Labarai24 da hausaloaded  ta yi ya tabbatar da cewa Sarkin Wakar yana nan cikin koshin lafiya kamar yadda wani makusancinsa ya tabbatar mana.


Ba wannan ne karon farko da ake samun irin wadannan labaran ƙaryar ba akan jaruman Kanywood ba, domin ko a cikin shekarar 2018 sai da aka yaɗa labarin cewa jaruma Sadiya Gyale, ta rasu. Haka shi Muhammadu Sani Idris Kauru wanda aka fi sani da Moda an yaɗa irin wannan jita – jitar a kan sa.
Akwai dai fiye da mutum miliyan 26 da suke amfani da shafin sada zumunta na Facebook a Najeriya, wannan dalili da kuma karuwar masu amfani da wayoyin hannu masu komai-da-ruwanka, na taimakawa wajen saurin yaɗa jita-jita a kafafan sada zumunta.
Hakan ne kuma ya sa ma’aikatar sadarwa ta ƙasar nan kaddamar da wani shiri na musamman domin yaki da wannan dabi’a, wacce ke kara samun gindin zama musamman a shafukan sada zumunta.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button