Advertisment
Ya fashe da kuka cikin wani karatunsa, yayin da yake bada labarin wani abu da ya gani, cewa wasu mutane suna sata ana tsaka da gobara a Cash and Cary.
Abinda malamin ya ce shin ta yaya za a yi nasara a haka?
A ranar Asabar ne wata gobara ta shi a wani katafaren shagon sayar da kayyaki Cash and Cary da ke birnin tarayyar Najeriya Abuja, wanda bayan tashin gobarar ne wasu mutane suka je suka yi wawaso kan kayan shagon.
Ƴan Najeriya dai na yawan sukan Fantami na rashin yin kuka a lokacin gwamnatin Buhari duba matsalolin ratshin tsaro da ya addabi yankin Arewacin Najeriya dama tsadar rayuwa.
Wanda acewarsu irin waɗanna matsaloli ne suka a baya shi ya Fantami ya dunga kuka a lokacin mulkin PDP.