Kannywood

Batun zubar da cikin Rahama Sadau, daga ina batun ya samo asali?

Labarin zubar da cikin jaruma Rahama Sadau, daga ina batun ya ke ne?

Advertisment

Wani mai jan hankali a dandalin TikTok kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta ruwaito, ya tura budaddiyar wasika ga Sheikh Isa Ali Fantami akan batun rufe TikTok, anan ya kara da yin wata magana dangane da Rahama Sadau da nufin a yi mata nasiha a kan wani abu da yake kokwanton kasancewarsa.

Amma ya ce ya kamata ko da gaskiya bane ya kamata a ja mata kunne.
Abinda malamin ke son a yi mata nasiha ko kuma yake zargin ance ta wallafa a kafar sada zumunta shine yadda a wata hira da aka yi da ita tace ita budurwa ce amma ba dal a leda ba kuma ta zubar da ciki sau da dama amma wai ba za ta iya boye hallayarta ta banza ba don hakan munafinci ne.

Akan wadannan maganganun ya ce a yi wa Rahama Sadau nasiha kuma dama kafin ya fara zancen ya fara da bayar da hakuri don ba lallai zancen ya kasance gaskiya ba, idan kuma gaskiya ne ta yi amfani da nasiharsa.

Advertisment

Mutumin ya ce ta yi wa addini mummunar fahimta, don duk mai boye fasikancinsa zai shiga aljanna idan ya nemi yafiyar Allah don irinsu akwai sa ran Allah ya yi musu rahama.
Bayyana barna haramun ne a musulunci, don ranar kiyama akwai wadanda Allah zai yiwa hisabi a boye, cikinsu akwai wadanda idan sun yi laifi ba sa bayyana laifinsu.

Ya ce tana yawan maimaita laifuka, don akwai lokutan da ta tafka laifin da har sai da aka koreta daga kungiyar ‘yan fim, kuma a kullum maimaita kuskuren take kara yi.

Ya kara da bayyana cewa ta tabbatar wa duniya cewa ‘yan wasan Hausa ba su cancanci su fadakar da jama’a ko suyi gyaran tarbiyya ba don su ma su na bukatar a fadakar dasu.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button