Datti Assalafy Yayi Zafaffan Tsokaci kan Rigimar Kannywood
Bayan yan rigimar da ta faru yan kwanan nan da ta faru a masana’antar kannywood wannan mawallafin yayi Zafaffan tsokacin da ya data kura a da wasu ke ganin bada kowa yake ba face jaruman masana’antar kannywood suna samu samabani yan kwanakin nan a shafinsa na sada zumunta koda bai wallafa hoto ba kuma bai kama suna ba, abinda ya wallafa a shaifinsa kamar haka.
“Fada Da Karuwai Da ‘Yan Luwadi Sai AN Shirya
Wata guzumar karuwa kuma ‘yar madigo a masana’antar shirya fina-finai ta sa an kama wani abokin sana’arta bayan ya zageta, yanzu haka yana kulle, kuma ita karuwan ta rufe layin wayoyinta
Tabbas nima Datti Assalafiy na kalli bidiyon da abokin sana’arta ya dura mata manyan zagi har da kalaman batsa ya jefeta dasu, saboda ta taba Maigidansu wanda shine ya fara sakata shiri film, tun ma bata iya hausa ba kafin tazo ta waye taci amanar maigidan nata
Bakuwar haure ce ‘yar cirani, ba ‘yar Nigeria bace, karuwanci ya kawota, yanzu tayi tasirin da har zata iya sa a kulle dan kasa, Allah Sarki
Mutane da yawa suna son suyi fada da karuwai musamman wadannan artificial karuwai na zamani amma basu san yadda zasuyi ba domin su tsallake tarkonsu
Wadannan karuwai da kuke gani jama’a musamman wadanda suke shirin film suna da alaka na lalata da manyan ‘yan siyasa da manyan Sarkuna, waya kawai zata daga ta kira Gwamnan garinku tace ina so a wulakanta min wane, shikenan an gama ba zai kwana a gida ba
Duk masu fada aji a cikin Gwamnati yawanci abokan huldar karuwai ne da suke film, kuma karuwan sun mallaki wasu hotuna da bidiyonsu na sirri wanda suka rike a matsayin makullin da suke juya shugabannin, a kowani lokaci suna tatsar kudi daga garesu, kuma karuwan suna sa suyi abu ko ba don Allah ba, saboda tsoron kada su fitar da sirrinsu
Ya kamata duk wani da yake da sha’awar yin fada da karuwai da sauran ‘yan iska to ya tsaya yayi karatun tuggun karuwai mai zurfi
A kaf duniyar facebook a Kasar Hausa babu wani marubuci da yaci mutuncin karuwai da ‘yan Luwadi kamar Datti Assalafiy, sun buga, sun hada sharrin da makirci, sun kada sun rawa amma sun kasa kai Datti Assalafiy kasa, saboda ban fara ba sai da na shirya, nayi karatunsu mai zurfi, facebook kawai ke taimakonsu ta hanyar kulle min account
Akwai rubutun da nayi kusan kashi 4 mai taken RAYUWAR KARUWAI CIKIN SIRRI duk me neman sanin sirrin karuwai da yadda suke sa masu iko su wulakanta abokan gabansu to ya binciko wannan rubutun, yana nan a Google Insha Allah
Allah Ka karemu daga sharrin karuwai da ‘yan Luwadi.”





