Kannywood

Duk Da Na Yi Aure Zan Ci Gaba Da Fitowa A Shirin Fim – Rahama M K

Tun bayan auren Fitacciyar Jarumar shirin Kwana Casa’in Rahama M K wato Fulani Matar Bawa Maikada, a watan daya gabata mutane suke ta tofa Albarkacin bakin su a game da auren nata da Kuma makomar ta a cikin harkar fim Musamman shirin Kwana Casa’in.
To sai dai Jarumar ta yi magana da Jaridar Dimukaradiyya a Karo na farko inda ta tabbatar da zata ci gaba da fitowa a harkar fim ba ma shirin Kwana Casa’in ba har ma da sauran finafinai da ta ke yi.
Jarumar ta bayyana cewar “Ai ita harkar fim kamar aikin Gwamnati ne ko kasuwanci da Matan aure su ke yi don haka zan ci gaba da yin fim tun da sana’a ta ce da na ke yi na ke samun kudi saboda auren na ba zai hana ni fitowa a fim ba.”
Daga karshe ta yi godiya ga dukkan mutanen da su ka yi Mata fatan alheri a game da auren da ta yi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA