Labarai

Wani Magidanci Ya Kama Matarsa Da Wani Kwarto Ta Hanyar Asiri

Masu neman matan aure sai ku tuba ku daina ganin yadda yanzu wasu mazan suke amfani da sirri domin cafke matansu da suke zargi da zina.
A yammacin yau ne wani ya turo mana hoto da labarin yadda wani magidanci ya kama matarsa da wani Kwarto a gidansu turmi da tabarya bayan da suka makale suka kasa rabuwa da juna.

Mijin daya yada hoton matar tashi yace ya jima yana zargin matarsa da kawo maza gidansu, zargin da matar tasa taki amincewa da shi. Yace har ‘yan uwanta ya koka musu amma suka nuna sharri yake nema yayi mata. Wannan ne ya hasalashi ya shiga neman asirin da zai kama mai zakkewa matarsa.

Wani Magidanci Ya Kama Matarsa Da Wani Kwarto Ta Hanyar Asiri
Wani Magidanci Ya Kama Matarsa Da Wani Kwarto Ta Hanyar Asiri

A wani bidiyon da aka aikomana wanda mijin ya dauka anga matar da kwarto suna kuka suna tuba da neman ya yafe musu ya rufa musu asiri.
Sai dai wasu da dama sunyi tir da matakin da wannan magidancin ya dauka na yayata matar tasa bayan suna da ‘ya’ya biyu. Inda wasu ke cewa da ya sake kawai tunda yana zarginta maimakon mata wannan tonon asirin.
Sai dai wasu na ganin ya kyau kuma yayi musu adalci da wannan matakin nasa na yadda bai aikasu barzahu ba.

Yadda neman matan aure da mata masu aure suke neman maza, zai tun zura wasu maza magidanta bin bokaye da matsafa domin neman kare aurensu ta ko wani hali. Wanda hakan na iya shafan imanin duk na mijin da yace zai yi hakan. Maimakon hakan yafi kyau kawai ka hakura da duk wata matarka da bakada natsuwa akanta.

Madogara : A Tonga

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button