Sako Zuwa Ga Gwamnatin Kano Gameda dakatar da Haska fim din Ta’addanci
Wasu jaruman masana’antar kannywood din da anka zanta da su a cikin wanann rahoto duk kamar suna nuna rashin goyon bayan abun kamar yadda zakuji a cikin faifan bidiyon da munka sanya.
Jaruma kuma uwa a masana’antar kannywood saratu gidado wato saratu daso itama ta fito ta gayawa duniya cewa tana goyon bayan wannan doka da hukumar tace fina finai dari bisa dari 100% dalilinta kuwa shine.
“kwarai naji dadin wannan doka takatar da nuna fim din shaye shaye a fim ko kidinafin ko kwacen waya dalili yara da muke da su karamar kwakwalwa ne da su zasu gani su kwaikwaya amma su manya daman sun san wannan wasar kwaikwayo ce.
Matsalar duk fina finai din da ake yi manya na kallo yaran na kallo saboda haka masu karamar kwakwalwa zasu koya. ”
Shima Ali Idris Muhammad wanda anka fi sani da ali artwork madagwal shima ya goyi bayan abun ga abunda yace.
” Nima ina goyon bayan wannan hukunci da Hukumar Tace fina finai ta yi duba da Addinin mu gaba yake da komai duk abunda zai kawo tabarbarewar tarbiyar da addinin mu ya koyar damu to barinshi shiyafi zama Alkhairi dan haka muna rokon Allah ta’allah ya shiryar da matasanmu da shuwagabanninmu, Allah ka zaunar da Kasar mu lafiya, Allah ya bamu ikon aikata dai dai, inda kuma Mukai kuskure Allah ka yafe mana baki daya.”