AddiniLabarai

Abdul-Jabbar Ya Tabbata cikakken Makaryaci, Babban Azzalumi, Kuma Katon Marar Kunya – Bulama Bukarti



NB: Ayi hakuri idan an ji kamar na kausasa lafazi yau. Manzon Allah (SAW) ya wuce haka.
Yanzu na gama sauraron tattaunawar da akayi da Abdul-Jabbar tun daga farko har karshe kamar yadda Freedom Radio ta saka. Bayan yayi ta koke-koken cewa ayi masa aldalci kuma yayi ta cika baki,, yau an ba shi wannan dama. Amma ya gaza amsa ko daya daga tambayoyin da akayi masa. Maimakon haka, sai yayi ta tsilla-tsilla. Da farko yayi ta karya cewa tambayoyin da aka yi masa basa cikin wandanda aka gabatar wa gwamnati. Da aka saka kaset din da aka kaiwa gwamnati kuma, sai ta fito cewa karya yake domin tabbayo biyu na farko da yace basa ciki, duk suna ciki 6oro-6oro. To, wai idan basa ciki ma, ba maganganunsa bane? Ba zai iya kare su? Wa yace sai wanda aka kaiwa gwamna zai amsa?

BulamA Bukarti

Bayan an kure anan kuma sai ya koma cewa wai minti goma ba zai isheshi ba. Kai da ka fadi littattafai da lambar hadisi da mujalladi da feji, amma kace ba za ka iya budo fejin hujjar ka ba? Daga nan kuma sai ya koma cewa wai so yake ya kare musulunci domin kada arna suyi mana dariya. Wallahi, ko baqaqen arnan farko basu jingina wa Annabi maganganun irin na Abdul-Jabbar, kuma shi ya kirkire su ba wani ba. Ga shi kuma baya iya cinye minti goman ma da aka bashi ba. To me ya hana shi amfani da mintunan da aka bashi kafin ya nemi kari? Amma kai da baka shanye kokon da yake kofinka ba, ka nemi kari? Kuma yaya akayi su abokan tattaunawarsa su ke bude hujjjojinsu, suna karantowa a mintin goman?
Wani karin abin haushi, ba na ce abin dariya ba, wai ai bai san alkalin ba, kuma ba shi fahimta ko alaqa da alkalin. Idan banda iskanci, wa yace sai kasan alkali zai iya yi maka Shari’a? Yanzu Magistrate din da aka gurfanar da shi a gabansa da kuma High Court din da ya kai kara wannan makon nan, duk ya san alkalan ne? A ka’idar Shari’a ma, idan kana da alaqa da alkali, to ba zai iya alkalanci akan maganar da ta shafe ka ba.
An bawa Abdul-Jabbar dukkan dama. Anyi masa aldalcin ya nema. Amma ya gaza kare maganganunsa. Ya buge da kewaye-kewaye da buge-buge da kame-kame. Tsilla-tsillan da Abdul-Jabbar yayi ya fi na kafirin da yayi an Ibrahim cewa “ana uhyee wa umeet” a Aya ta 258 a Suratul Baqara. Ta tabbata cewa Abdul-Jabbar shi ya kirkiri wadannan maganganu. Karya ya yiwa Allah da ManzonSa. Ya zalunci ilimi, ya zalunci al-ummar musulmi, ya zalunci Allah da ManzonSa. Amma bai zalunci kowa ba face kansa.
Har zuwa yau ban ta6a cewa koma akan Abdul-Jabbar. Amma yau an ba shi damarsa. Wallahi, na dade ban ji makaryaci, maras kunya irin yadda Abdul-Jabbar yayi yau ba. Wannan mutumin babban hatsari ne a cikin al-umma. Ta tabbata shi ya kirkiri maganganun da yake jingina wa Manzon Tsira (SAW). Ko mabiyansa sun san ya fadi warwas. Ko tambaya daya bai amsa ba. An kure Abdul-Jabbar kaf! Wannan mutumin ba shi da wani sauran uzuri. Kowa yana da ‘yanci addini, amma ba wanda yake da ‘yanci gur6ata addinin mutane ko kuma ya haifar da tashin hankali.









Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button