Addini
Karamomin Shehu Nyass Ne Silar Arziki Da Ilimin Sheikh Isiyaka Rabi’u -Sheikh Dahiru Bauchi
Malam Isyaka Rabi’u Shi Kadai Allah Ya Yi Wa Wata Kyauta A Almajiran Sheik Ibrahim Nyass Da Babu Kamarsa A Nijeriya.
Sheik Dahiru Bauchi ya ce “Ka bada darrusan karatun Kur’ani, sannan ka tafi ka bude kanti (kasuwanci), Sannan ka dawo ka bude wazifa a Zawiyyarka. Sannan ka hidimtawa ‘ya ‘yan Shehunmu Shehu Ibrahim RTA.
“Mu mahaddata mun yi rashin dan uwanmu mahaddaci, mun ‘yan Tijjaniya mun yi rashin dan uwanmu dan Tijjaniyya, masu kudi sun yi rashin dan uwansu mai kudi.
“Ina yi wa gwamnatin Kano da masarautar Kano ta’aziyya. Allah ya gafarta masa”.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com