Kannywood

Aisha Dan Kano ta tafi ta dawo, yadda Zee Dan Kano ke shirin maye gurbin mahaifiyar ta

Advertisment

Aisha Dan Kano ta tafi ta dawo, yadda Zee Dan Kano ke shirin maye gurbin mahaifiyar taKamar yadda bayan rasuwar Marigayi Rabilu Musa Ibro, dan sa mai suna Hannafi Rabilu ya daura damarar maye gurbin sa, alamu na nuni da cewa marigayiya Aisha Dan Kano ma za ta iya samun mai gadon ta idan hali ya yi.
A ‘yan kwanakin nan wasu bidiyo suka fara yawo a shafukan Instagram da tiktok na wata matashiya mai tsananin kama da Aisha Dan Kano, wacce ke yin koyi da muryar ta.
Kamannin wannan matashiya mai suna Zee Dan Kano dana marigayiya Aisha Dan Kano ya yi yawa sosai, inda hakan ya sanya ya dauki hankulan al’umma suka dinga mamaki, sai dai kuma bayan bincike da Tashar YouTube ta Tsakar Gida ta yi ta gano cewa Zee diya ce ga marigayiya Aisha Dan Kano.

Duk da dai Zee ba ta nuna ra’ayi na maye gurbin mahaifiyarta ba alamu na nuni da cewa inda za ta yi hakan za ta bada kwafin mahaifiyarta kwabo da kwabo, sai dai kuma mafi yawan tambayoyin da ake yi mata a shafin ta kan za ta fara fim ne? ba ta bada amsa ba.
 
Duk da dai Zee ba ta nuna ra’ayi na maye gurbin mahaifiyarta ba alamu na nuni da cewa inda za ta yi hakan za ta bada kwafin mahaifiyarta kwabo da kwabo, sai dai kuma mafi yawan tambayoyin da ake yi mata a shafin ta kan za ta fara fim ne? ba ta bada amsa ba.
 
 
Amma tambayoyi da suka shafi dangantakarta da Aisha Dan Kano, ta bada amsa da cewa mahaifiyarta ce, inda mutane da dama suka dinga addu’ar fatan rahama ga mahaifiyarta.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button