Labarai

Kaduna: An Tsige Limamin Da Ya Yi Kiran A Daidaita Sahu A Masallaci

Rahotanni daga Jihar Kaduna sun bayyana cewar an tsige babban limamin masallacin juma’a na ‘yan lilo dake Unguwar Tudun Wada Kaduna, biyo bayan karya dokar gwamnatin jihar da ya yi akan CORONA.

Limamin mai suna Malam Musa Assalamu Alaikum, ya umarci mutane a ranar juma’a da cewar su shigo cikin masallaci kowa ya haɗa sahu da kafaɗa, lamarin da ya haifar da guna guni tsakanin wasu jama’a, inda malamin ya bayyana cewar babu dalilin yin salla jama’a na nesa da juna dole a kusanci juna, kuma babu wanda zai iya dakatar da shi daga bin tsarin da addini ya gindaya sai dai idan sauka zaiyi daga limancin.

Bayan zaman da kwamitin masallacin ya yi ƙarƙashin jagorancin shugaban kwamitin Alhaji Ibrahim Husaini wanda Kwamishina ne na muhalli a jihar, an yanke hukuncin tsige limamin daga limanci saboda cin karo da dokokin kariya daga CORONA da ya yi.

Gwamnatin jihar ƙarƙashin Gwamna El Rufa’i tuni ta sanya sharadi ga duk masallacin da aka samu da karya dokar, ko dai a rusa Masallacin ko kwace lasisin masallacin ko a tsige Limami

Shafin Nijeriyarmu a yau na Wallafa wannan labari.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button