Addini

Yaro dan shekara 8 mai tafsirin Al-qur’ani

Advertisment

Latsa wannan hoton na sama domin kallon hira da malam

Muhammad Shamsuddeen ya zamo wani abin misali a duniyar Musulmi ta yau kasancewar yana daya daga cikin yara masu karancin shekaru da suke nuna bajinta a fagen ilmi.

Malamin mai shekara takwas da haihuwa ya ce ya fara makaranta ne bayan da aka yaye shi.

Yanzu dai baya ga tafsirin al-qur’ani, Shamsuddeen ya sauke littafai kamar Kawa’idi da Ahlari da Risala da Ishamwiy da Mukhtasar da dai sauransu.

Malamin kan hau kujerar mahaifinsa ta bai wa manya karatu ko kuma tafsirin al-qur’ani mai girma a watan Ramadan.

Sai dai duk da cewa Muhammad Shamsuddeen ya zama shehin malami a fagen addinin Musulunci, burinsa shi ne kasancewa lauya a nan gaba.

Mun dauko wannan tattaunawa daga bbchausa

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button