Addini

‘Yan Hakika Ba ‘Yan Tijjaniyya Ba Ne Yan Shedaniyya Ne, Inji Sheik Dahiru Bauchi

…kaf Nijeriya babu wanda ya kai mabiya Tijjaniyya yawan mahaddata Kur’ani, cewarsa

Daga Babangida A. Maina

Sheik Dahiru Bauchi ya ce

“Akwai Musulmi Da Yawa Suna Shan Giya, Suna Neman Mata, Suna Sata, Suna Karya, Suna Luwadi, Suna Caca, Suna Madigo, Suna Aikata Laifuka Mabanbanta Wanda Aka Sani Da Wanda Ba’a Sani Ba.

Shin Musulunci Ne Ya ce Su yi Hakan? Kowa Zai ce Mun A’a.

To Haka Abin Yake a Wajan Wasu Mutane Masu Kiran Kansu Da ‘Yan Hakika a Cikin Tijjaniyya Dukkan Abubuwan Da Kuka Ga Suna yi Ba Tijjaniyya Ne Ta Koya Musu Ba, A’a Su ‘Yan Shedaniyya Ne.

Ga Abinda Tijjaniyya Ta Koyar Kamar Haka;
* Istigfari,
* Salatin ANNABI (S.A.w), Da
* Lailha Illallahu,
* Kulawa Da Sallahn Jam’i,
* Girmama Iyaye Da Yimusu Biyayya,
* Yawan Karatun Qur’ani.

Shine Aikin ‘Yan Tijjaniyya. Shi ya sa a Nijeriya Babu Wanda Ya Kai ‘Yan Tijjaniyya Na Gaskiya, Ba Tijjaniyya Bogi Ba, Yawan Mahaddata Alqur’ani.

Ya Kamata Sauran Jama’a a Dunga Mana Adalci”.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button