Taƙaitaccen Tarihin Sheikh Abdul-Rahma Ibn Abdulaziz Wanda Ankafi Sani Da Al -Sudais
Daga Musa Badayi
Cikkaken sunan sa shi ne Shiek Abdul-Rahman Ibn AbdulAziz As Sudais. An haifishi a shekarar 1960, a Riyard, babban birnin kasar Saudi Arabia, ya fitone a daga cikin wani jinsi mai suna Anza. Al Sudais, ya haddace Alkur’ani, ya na dan shekaru 12, ya kuma kammala karatunsa na makarantar Sakandiri, a shekarar 1979, ya kuma kammala digirinsa, a fan nin Sharia, a shekarar 1983, ya yi wan nan digirinne a wata jami’ar Musulunci da ke Riyard, babban birnin Saudi Arabia.
Ya yi digiri na biyu, wato (masters), a cikin shekarar 1995, kuma ya yi digirin digirgir (Doctorate), duk a fannin Sharia. Ya yi aiki a jami’ar da ya kammala ta Riyard, San nan ya yi aiki a a jami’ar Ummal Qura, a matsayin mataimakin Farfesa. An zabe shi ya zama limamin babban Masallacin Makka, ya na da shekaru 24, kachal, ya kuma yi hudubar sa ta fari ya na shekaru 24, a cikin watan july cikin shekarar 1984. A cikin shekarar 2012, ya zama babban mai kula da babban masallacin Makka, kuma aka ba shi mukamin minista.
Join Our WhatsApp Channel
Get verified job vacancies, career tips, scholarships and opportunities delivered straight to your phone, free and as soon as they're posted.





