Hassada ce Ta sa Aka la’anci Rahama sadau aka ki yiwa Sahara reporters – Jaruman kannywood
Mawaki kuma jarumi amad abdallah wanda aka fi sani da excellency a cikin shirin labarina ya sake fitowa akan batancin da sahara reporters nayiwa Annabi Muhammad s.a.w.
Jarumin yayi bidiyo tare da rubutu akan irin hassada da anka nuna akan rahama sadau da yanzu kuma an kama baki anyi shiru.
Ga bidiyon nan kasan rubutun bayan kamala karantawa sai ku saurara.
“Kuna iya yamadidin tallata wakokin ku, wasanni, fina-finai, hotunan zubda mutunci, kuna bata lokaci wajen Posting abubuwan zubda mutunci da Sunan wayewa da Sunan ku celebrities ne, amma sau daya bazaku iya kare martabar Annabi SAW, wanda kuke karyar saka wakoki da raye-raye da sunan soyayyar sa, wannan abun kunya ne, ace duk tarin followers dinku babu kason Allah da manzonsa a ciki, yauda munafurci ne da kin juna ko wani abu ya samu wani ana yayatawa saboda Hassada.
Kiyi hakuri @rahamasadau Allah yasani sanda matsala ta faru dake ba kinki nake ba, bal ma kinsan irin kaunar da nake Miki tasa na gaya miki gaskiya, domin ke amintacciyata ce, na dauka lokacin da akayi miki ca son Annabi SAW ne yasa akayi miki haka, amma sai yanzu na gane da yawansu tsabar hassadace da kin jininki, kama daga wanda suka dunga kukan karya da munafurci, da masu la’antarki ashe duk hassada ce ta motsa ganin ni’imar da Allah ya miki, duk da cewa kinyi kuskure ta wani bangaren amma gaskiyar itace idan har kina musulma za’a kasa miki adalci, to ina ga wasu kafirai makiya Allah, makiya zaman lafiyar kasarmu.
Ku kuma bazamu fasa gaya muku ba, koda kurame zaku zama saimun gaya muku gaskiya, ko kuna so ko bakwa so. Hakuri yayi mana kadan… muhammadubuhari @buharisallau @bashirahmaad @mrs_indmi hanan_buhari @profosinbajo @musahalilu @umarkhan__nuhu
#saynotosaharareporters #saynotosaharareporters.”


