Yan uwa Musulmai A taimakawa musulmi Jarumi Sk yana Neman taimako


Ga bainda ta wallafa a shafinta
“WASU DAGA YAN FIM SUN TAIMAKAWA SANI SK
Mutane suna ta turo min wannan video na Sani Sk akan mu taimaka masa, to magana ta gaskiya a kwanakin baya ma mun yi posting Sani Sk kuma wasu daga cikin yan fim sun taimaka masa kuma suna kan ci gaba da taimala masa da al’umar gari, sai dai cutar shi mai cin kudi ce wato ciwon sugar da ciwon hanta.
Yanzu haka @abdulamart_mai_kwashewa ya Bashi Dubu Dari biyar, ya sa kuma an kai shi asibiti, Hadiza Gabon ta bashi Dubu Dari Biyu da Hamsin, Ali Nuhu ya bashi Dubu Dari, Aisha Tsamiya Dubu Dari, da wasu da yawa da suka bayar daga masana’antar Kannywood din, muna adduar Allah ya saka musu da alkairi.
Kamar yadda muke fada ciwon Sani Sk ciwo ne mai cin kudi, Yan fim suna iyakacin kokarinsu, amma kuma al’umma dan’uwanku ne musulmi Wanda wannan yan’uwantakar ta fi ta sanaa za ku iya taimakawa ba tare da cin mutunci kowa ba.
Allah ya ba shi lafiya.”
View this post on Instagram





