Kannywood

Kidnappers da Taron Biki Ya kamata Hankalin Masu Sarar kaba Ya koma Ga Rina ~ Falalu Dorayi

Advertisment

Kidnappers da Taron Biki Ya kamata Hankalin Masu Sarar kaba Ya koma Ga Rina ~ Falalu Dorayi
Kidnappers da Taron Biki Ya kamata Hankalin Masu Sarar kaba Ya koma Ga Rina ~ Falalu Dorayi
Hoto :Facebook

Fitacen jarumi kuma mai shirya fina finai da bada umurni falalu dorayi yayi magana akan harkat masu garkuwa da mutane da kuma yadda ankayi bukin dan shugaban kasa Muhammadu buharina shafinsa na sada zumunta.
Ga abinda ya wallafa.
“An gama biki, Ido ya gani duk wani Babban mai kudi, Basarake, ‘Yan siyasa, Ma’aikatan Gwamnati, da Manyan masu ‘Damara da suke Arewa sun halacci taron bikin da akai a Bichi. Allah ya bawa ango da amarya zaman lafiya.
Har Yanzu akwai daruruwan al’umma mata da maza, yara da Manya a jeji hannu kidnappers.
Wasu garuruwa tuni sun hakura da noma.
Kisa rai da karbar kudin fansa kuwa, kullum karuwa yake a arewa.
Ina ma a ce yadda kuka taru a Bichi dauren aure, Ku gwada irin taron akan matsalar satar mutane da take addabar arewa, a kankanin lokaci sai kaga kun samo karshen matsalar.
Ran mutum baya bukatar a yi siyasa dashi. Da zaku ajjiye differences da ke tsakanin ku, ku dauki matsalar talaka matsalarku, sai kaga kun kawo mafitar Kisan kai, cin zarafin, Fyade, da Yan Ta’adda sake wa Al’ummarku a arewacinmu.
Tsakani da Allah dai Ya kamata
HANKALIN MASU SARAN KABA YA KOMA GA RINA.
Allah ya bamu zaman lafiya, ya shiryamu ya bamu Jagorori nagari. Amin.
Jum@tMbrak #sisters & #brothers
#falaluadorayi”

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button