Ga ni da rai na, ban mutu ba- Cewar Samanja
A YAU Alhamis aka wayi gari da labarin wai shahararren ɗan wasan kwaikwayo ɗin nan, Alhaji Usman Baba Pategi, wanda aka fi sani da suna Samanja Mazan Fama, ya rasu.
To amma mujallar Fim ta zanta da shi, inda ya ƙaryata labarin.
Labarin ya bazu a soshiyal midiya ne bayan wani tsohon darakta a Hukumar Talbijin ta Ƙasa (NTA) ya rubuta a shafin sa na Facebook cewa Allah ya yi wa Samanja rasuwa.
Nan da nan fitaccen ɗan jaridar nan Ibrahim Sheme ya sanar da wanda ya yi rubutun da kuma jama’a cewa Samanja dai na nan da ran shi.
Sheme ya ce a matsayin sa na wanda ke rubuta tarihin rayuwar Samanja shi da ma’aikacin gidan talbijin ɗin nan na KSTV da ke Kaduna, wato Sgafi’u Magaji Usman, ya na bada tabbacin cewa Samanja na nan da ran sa.
Sheme, wanda sanannen marubuci ne, ya ce sun yi magana da Samanja da iyalin sa jim kaɗan bayan sun karanta wannan labari da aka ƙaga a Facebook.
Karanta kuma Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raj’un: Allah Yayiwa Fitaciyar jarumar kannywood Rasuwa
Ya ce bai kamata wanda ya ƙaga labarin ya tura irin wannan saƙo ba tare da ya tabbatar da ingancin sa ba.
Wanda ya fara bada labarin dai ya ɗauki gyara ba tare da ɓata lokaci ba, kuma ya goge rubutun nasa tare da bada haƙuri.
Sai dai kash! labarin ya ci gaba da yaɗuwa a shafuka da guruf-guruf na soshiyal midiya.
Saboda haka ne dai abokin aikin Sheme, wato Shafi’u Magaji Usman, ya garzaya zuwa gidan Samanja da ke unguwar Kabala Costain a Kaduna, inda ya tattauna da tsohon ɗan wasan domin kawar da ji-ta-ji-tar.
A hirar tasu, Alhaji Usman Baba Pategi ya bayyana cewa shi dai ya na nan da ran sa bai mutu ba.
Ya ce, “Mutum da ran shi, ga shi ina magana ma da kai, ko ba haka ba ne? An taɓa ganin wanda ya mutu ya na magana da wani? Ba zai yiwu ba! Mutane ne dai kawai! Mutum ne kawai – ko mai son ka ne, ko maƙiyin ka ne!”
Karanta kuma Lukman Na Shirin Labarina Ya Bayyana Alakarshi Da Nafisa Abdullahi
Samanja ya ce duk abin da Allah ya ƙaddara wa bawan sa, shi zai same shi.
Shi dai Alhaji Pategi, ya fara wasan kwaikwayo tun bayan dawowar sa daga Yaƙin Basasar Nijeriya, inda ya yi aikin soja, kuma ya ci gaba da gudanar da wasan ‘Samanja Mazan Fama’ da na ‘Duniya Budurwar Wawa’ har zuwa lokacin da ya yi ritaya saboda halin manyantaka da kuma rashin isasshiyar lafiya.
To Allah ta ba shi lafiya da ƙarin rayuwa mai albarka, amin.