Kannywood

Lukman Na Shirin Labarina Ya Bayyana Alakarshi Da Nafisa Abdullahi

Lukman Labarina, wato Yusuf Muhammad Abdullahi wanda kuma ake kira da Yusuf Saseen na cikin fitaccen shirin nan mai dogon zango wato Labarina, ya bayyana babban burin shi a nan gaba a harkan wasan kwaikwayon da yake gudanarwa a yanzu.
A wata tattaunawa da BBC Hausa cikin shirin nan nasu na daga bakin mai ita,yayinda Lukman Labarina ya bayyana cewa babban burin shi a harkar film shine yaga sunyi abinda jama’a zasu riƙa koya daga gurin su.

Lukman tare Da Sumayya a cikin shirin labarina

“Burina na gaba a rayuwa shine wannan harka da muke yi ta film, ya zamana cewa muna yin abinda ya dace a ciki wanda zai ringa taɓa rayuwar al’umma mutane suke koya daga cikin abinda muke yi, gaskiya wannan shine babban burina.”
Lukman labarina ya kuma bayyana cewa ya fara harkar film ne a shekarar 2017 bayyan kammala yima ƙasa hidima da yayi a Keffi jihar Nasarawa. Ya ce ya fara ne da wani film mai suna Camfi.
Kamar yadda arewamobile ta ruwaito cewa, An tambaye shi ko menene alaƙar shi da Nafisah Abdullahi wacce aka sani da Sumayya a cikin shirin labarina, sai Lukman ɗin yace Sumayya abokiyar shi ce, aikinsu iri ɗaya a cikin film, ƴar film ce ita, shima kuma ɗan film ne. Sai dai kuma yace a bayan fage kuma ƙawar shi ce.
Sannan Lukman labarina ya bayyana cewa abinda yafi burge shi a harkar film da yake yi shine yadda tauraruwar shi ta haska cikin sauri dukda cewa wasu na ganin bai shigo harkar da wuri ba. Ya ce akwai garin da yaje ɗaurin aure, bai samu damar fita ba har saida ƴan sanda suka zo saboda yawan masoyan sa a gurin.
Shirin labarina dai shiri ne mai dogon zango da a can baya yake zuwa a duk sati-sati a gidan talabijin ɗin Arewa 24. Zuwa gobe juma’a, 02 ga watan Yuli 2021 ne dai ake sa ran cigaba da haska shirin na labarina.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button