Kannywood

Nafisa Abdullahi ta yi kaca-kaca da wata me yunkurin yin kwacen saurayi

Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta caccaki wata da ta zarga da yunkurin kwacen saurayi duk da yangar da take wa maza.
Nafisar ta saka wani sako a shafinta na Twitter da ta rubuta cewa, Kina ta wani yanga amma kin koma gefe kina kokarin yiwa kawarki kwacen saurayi, kina rokon abubuwan da kike nunawa Duniya cewa kinfi karfinsu, kina ta yanga kamar ke wata ce, yanzu kallon huhun ma’ahu nike miki. Ba kima sai kai kai inda Allah be kai mutum ba.
Nafisar dai bata bayyana ko da wa take ba amma masoyanta da dama sun rika bata baki a shafin nata yayin da wasu suka rika tambayar wa ya tabota?

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button