Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raj’un: Allah Yayiwa Fitaciyar jarumar kannywood Rasuwa
A cikin daren ne muka samu labarin Allah yayiwa fitaciyar jarumar kannywood rasuwa hajiya zainab booth uwar jaruman masana’antar fim Ramadabooth, maryam booth da amude booth
Kamar yadda kannywood celebraties sunka wallafa a shaifinsu kamar haka.
“Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raj’un
Allah ya yi wa fitatciyar Jarumar Fina Finan Hausa Hajiya Zainab Booth rasuwa. Muna rokon Allah ya jikanta ya gafarta mata. Ya kuma yafe Dukkanin kurakuren ta Ameen ya Allah ?
#kannywoodcelebrities #kannywood #kancelebnigeria”
Sanarwa Inda za’ayi Jana’iza kenan daga shafin Jarumin Ali Nuhu
Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raj’un Allah yayiwa Haj Zainab Musa Booth rasuwa, gobe za a yi jana’iza a gidan ta da ke kallon Premiere Hospital a Court Road da karfe takwas na safe (8:00am). ALLAH ya jikanta da rahama, ya sa aljanna ce makomarta, amin.
One Comment