Yadda Aboki Ya Kama Abokinsa Tsirara Zai Yi Lalata Da Matarsa A Garin Katsina
An Kama Wani Magidanci Yaje Kwartanci A Gidan Babban Abokinsa, Da Ke Modoji, A Cikin Birnin Katsina
Wani magidanci ya kama abokinsa tsirara, yaje kwartanci gidansa a Unguwar Modoji, cikin birnin Katsina, amma an sakaya sunan Abokin da kuma wanda yaje kwartancin, kamar yadda shafin Alfijir hausa na ruwaito.
Shaidu sun tabbatar ma Katsina Post cewa “wanda aka kama ɗin abokine na kut-da-kut ga wanda aka je wa kwartancin wajen matarsa”.
Lamarin dai ya faru ne ranar Lahadin da ta gabata da marece.
Mun samu labarin cewa kwarton ya dade yana neman matar abokin nasa, amma ta ki bashi haɗin-kai, har ma ta kai ga ta faɗawa mijinta.
Sai dai mijin da farko bai yadda ba, saboda ganin irin alakar da ke tsakanin su da abokinsa, har sai daga baya ya yarda da maganar matarsa.
Wani abokin mijin ya bayyana cewa “matar ta daɗe tana faɗawa mijinta cewar “abokinka yana yi mini maganganun banza har ma yana nemana ta hanyar banza”.
“Amma shi mijin ya musanta kalaman matar, saboda kallon irin alaƙar abotar da ke tsakanin su”. inji wani abokin mutanen biyu da ya bukaci a sakaya sunansa.
Abokin ya cigaba da shaidawa Katsina Post cewa “ranar da dubun kwarton ta cika, magidancin ne ya faɗawa abokinsa cewar yayi tafiya, amma sai ya laɓe a cikin Silin, sannan ya haɗa baki da matarsa a kan ta kira kwarton, kuma ta ja hankalinsa har ya cire kayan jikinsa”.
“Hakan kuwa na faruwa sai magidancin ya fito daga maɓoyarsa, sannan ya yi kururuwa, abokansa suka shigo gidan inda suka kama shi tsirara”.
Haka dai suka yi ta bugun kwarton, sannan suka lalata mashi mashin ɗinsa roba-roba da ya je kwartancin da shi, kafin daga bisani su kai shi a wurin ‘yan sanda”.
Allah ya tsare mu daga mummunar ƙaddara, Amin.