Labarai

Komawata Addinin Musulunci Ra’ayi na ne – Cewar Mawakiyar da to Koma Addinin Musulunci

Wata fitacciyar mawaƙiya ‘yar ƙasar Saliyo mai suna Swadu Natasha Beckley ta karɓi addinin musulunci, inda ta kuma bayyana cewa ra’ayin ta ne ta karɓi addinin tunda ta ga shi ya fiye mata.

Komawata Addinin Musulunci Ra'ayi na ne - Cewar Mawakiyar da to Koma Addinin Musulunci
Komawata Addinin Musulunci Ra’ayi na ne – Cewar Mawakiyar da to Koma Addinin Musulunci

A rana juma’a, 28 ga watan Oktoban da ya gabata ne dai mawaƙiyar ta wallafa a shafin ta na Facebook inda ta sanar da cewar ta koma addinin musulunci.

Sama da shekara ɗaya tana son karɓar musulunci

Ta ƙara da cewar sama da shekara ɗaya tana ta son ta komawa addinin Musulunci, kuma yanzu tunda ta musulunta zata yi ƙoƙarin ganin cewa ta koyi duk abubuwan da suka kamata ta koya, duk da dai cewa akwai abubuwa da yawa da ya kamata ta koya.

“Na karɓi addinin Musulunci a wannan juma’ar. Zanyi bayani nan bada jimawa ba, amma na kai tsawon shekara ɗaya da wata ɗaya ina ƙoƙarin ganin cewa nayi hakan.

“Shi yasa a wannan juma’ar kawai na yanke shawarar hakan. Duk da dai nasan da cewa ba’a dare ɗaya zan koyi komai da ya danganci musulunci ba, amma lallai zanyi iya bakin ƙoƙarina wajen ganin na koyi abubuwan da suka kamata.” inji mawaƙiyar.

An caccaki nawaƙiyar kan yanayin shigar ta

Mutane da dama sun caccake ta kan yanayin shigar ta da yadda take fitowa, sai dai mawaƙiyar tace da da sannu-sannu zata koyi komai da komai da ya kamata ta koya na addinin Muslunci.

“Ku saurara kuji, wannan sabuwar hanya ce dana ɗauka kuma nake sanar daku. Da sannu-sannu ina ƙara koyon yadda ake gudanar da addinin. Amma ina son ku sani cewa, ra’ayin ku ako da yaushe zai zama na ku ne ba nawa ba. Wannan ni ra’ayina ne da na zaɓar kaina don na cigaba da kasancewa a ciki.

Ƙungiyoyin addinin musulunci sun yaba mata

Kungiyoyi da dama na addinin musulunci sun yaba ma mawaƙiyar bisa ƙoƙarin da ta yi na karɓar addinin inda suka riƙon Allah ya tabbatar da ita akan hanya madaidaiciya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button