Labarai

Na Dakatar Da Haihuwa Haka, a Cewar Wani Mai Mata 12 Da ‘ya’ya 102 Da Kuma Jikoki 568

Wani manomi ɗan kasar Uganda wanda ke da yara 102 da jikoki 568 da ya samu daga matansa 12 da ya aura ya yanke shawarar daina haihuwa.
Ɗan kasar Ugandan mai suna Musa Hasahya mai kimanin shekaru 67 a duniya ya bukaci matansa da su fara amfani da magungunan hana daukar ciki don su samu su din ga cin abinci. Dimokuraɗiya na ruwaito.Na Dakatar Da Haihuwa Haka, a Cewar Wani Mai Mata 12 Da ‘ya’ya 102 Da Kuma Jikoki 568

Jaridar The Sun ta rawaito Musa yana cewa: “Kudaden shigana na kara yin baya a ‘yan shekarun nan saboda tsadar rayuwa kuma iyalina na kara haɓɓaka. Ina ta auren mata ɗaya bayan ɗaya. Ta yaya namiji zai gamsu da mace daya. Dukkaninsu matana nawa na zaune ne tare a gida ɗaya. Ya fi mun saukin lura da su da kuma hana su hulɗa da sauran maza a kauyen nan.”
Zulaika wacce ta kasance amarya ga Musa Hasahya ta ce ta haifa masa ‘ya’ya 11:
“Ba zan sake haihuwar ‘ya’ya ba. Na ga mummunan yanayi na rashin kuɗi kuma yanzu ina shan maganin hana ɗaukar ciki.”

Na Dakatar Da Haihuwa Haka, a Cewar Wani Mai Mata 12 Da ‘ya’ya 102 Da Kuma Jikoki 568
Na Dakatar Da Haihuwa Haka, a Cewar Wani Mai Mata 12 Da ‘ya’ya 102 Da Kuma Jikoki 568

Musa da iyalinsa gaba ɗaya na zaune ne a Lusaka da ke kasar Uganda inda aka halasta auren mata da yawa.

Sai dai kuma akwai takaddama sosai game da shan kwayoyin hana ɗaukar ciki kuma a kan alakanta shi da lalata.

Kimanin kaso uku na yaran Musa suna rayuwa da shi ne a cikin gonarsa.
Karanta Wannan Labaranin

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button