Labarai

Mulkin Mallaka: Yari Ya Mayar Musu Jihar Zamfara Gidan Yari Budaddiyar Wasika Ga Shugaban Kasa.1. Shekara kusan bakwai Yari bai taba daukar ma’aikata ba.
2. Shekara kusan bakwai duk wata sai Yari ya zubar da ma’aikata.
3. Cikin shekarunsa bakwai ba ya iya biyan mafi karancin albashi, akwai ma’aikatan da ke daukar Naira 7,000 da kuma masu daukar Naira 6,500.
Tsawon wannan shekaru bai taba biyan kudin hutu ba (leave grants).
4. A duk tsawon wannan shekarun Yari bai taba biyan kudin shekara ba (Annual increament)
Kana kuma ba a taba yi wa ma’aikaci karin matsayin ba (Normal civil servant promotion)
5. Sannan akwai albashin ma’aikata sama da 1,300 da har yanzu ba a biya su albashin kusan watanni 36 ba.

6. Ma’aikata da dama da su ka yi ritaya, ba fansho ba garatuti, ta yadda da dama ko kudin asibiti ba za su iya biya ba.
7. Manyan asibitoci a kananan hukumomi 14 su na cikin mummunan yanayi ta yadda kowacce asibiti likita daya ne ya ke ganin majinyata kusan marasa lafiya 100 a rana.
8. Kotuna sun zama kufai sakamakon rashin albashi da sauran hakkokin ma’aikata ta yadda wasu ko shigar da kara an daina.
9. Tallafawa matasa da gwamnatin baya ta rika yi a a baya yanzu ya zama tarihi a lokacin Yari.
10. Dalibai sun manta da wani tallafin karatu da a baya a ke ba su, wanda yanzu da dama sun fara hakura da muradin karatu a jihar Zamfara.

11. Manyan mukamai duk ya rabe a karamar hukumarsa. Misali; kananan hukumomin Maradun da Birnin-Magaji kowacce babban sakatare (Permanent secretary) daya ne da su, amma karamar hukumarsa Talata-Marafa guda 9 ya nada. Haka ma sauran manyan mukamai gaba-daya ya tattare a garinsu kamar dama can ya ke mulka ba kananan hukumomin Zamfara 14.
12. Gwamna Yari da ’yan majalisar dokokin jihar sun hada kai sun mayar da kasafin kudin jihar abin boyewa daga sauran ’yan jihar. Su yi yadda su ka so ba tare da bin doka da oda ba.
13. Tun da a ka rantsar da Yari a matsayin gwamnan jihar Zamfara ya ki biyan ’yan kwangilar da su ka gama ayyukansu.
14. Yari ya kan bayar da kwangilar son rai ba tare da an bibiyi yadda a ka kashe ko fitar da kudaden ba. Misali; ya bayar da aikin titi mai hannu biyu a garinsu kan kudi Naira Bilyan 10 kuma mai tsayin kilomita 28.
15. ’Yan Majalisar Zamfara sun zama KURAME, BEBAYE kuma MAKAFI tunda ya saya mu su motocin alfarma (2016 Ford Escape SUV) na kimanin Naira miliyan 18 kowacce.
16. ’Yan kasuwa ba a maganarsu, don ya kai su kwandon shara; baya kula su balle ya taimake su.
17. Dalibai sun gama SS3, sun yi WAEC da NECO, amma idan ba ka yi sa’a ba sai shekara mai zuwa za ka samu jarabawarka.
18. Gaba dayan jihar Zamfara kwararrun likitocinmu (consultants) guda biyu ne kacal; asibitoci ba ma’aikata bare magunguna.
19. Babu tsaro a cikin jihar Zamfara. Kauyukan jihar kullum sace-sace da fashi da garkuwa da mutane a ke yi; rayuka sai salwanta su ke yi.

Mu na kira ga shugaban kasa ya kawo ma na dauki; yunwa, talauci da fatara na neman kashe mu. Da alama Yari ba ya tausayin talakawan jihar Zamfara. Ya fi kama da dan mulkin mallaka maimakon dan siyasa. Ba ya ji ba ya kuma gani, kamar yadda kalamansa ke nuna ba shi da tausayi.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button