LabaraiUncategorized
Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yabawa Minista Pantami Da Ya kai masa Ziyara (Hotuna)


Advertisment
Mai girma ministan sadarwa da tattalin Arzikin Zamani, Sheikh Dakta Isa Ali Pantami ya kai ziyara ga jagoran Darikar Tijjaniyya a Nijeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi a yau jumma’a 11/06/2021, a garin Bauchi.
Yayin ziyarar shehin malamin ya yaba wa minista Pantami, kuma yace a iya sanin shi, shine malami na farko kuma mahaddacin Alqur’ani da ya zama minista a Nijeriya.
Akarshe shehin malamin yayi addu’a ga minista da kuma kasa Nijeriya.