Yan Boko AQeedah Ga Aiki Ya Sameku ! Dan Shekara 10 Ya Dirkawa Yar shekara 13 Cikin Shege (Hotuna)
‘
Daga : Datti Assalafy
Wata yarinya ‘yar Kasar Rasha mai suna Darya Sudnishnikova ‘yar shekara 13 da haihuwa, ta bayyana cewa wani yaro mai suna Vanya ‘dan shekara 10 ya dirka mata ciki
A watan daya na wannan shekara 2020 Darya ta bayyana cewa Vanya ne ya bukaci muyi lalata, ni kuma ban damu ba, sai ya rufe kofar dakin da muke ciki sai ya bar makulli a jikin kofar saboda kada mahaifiyarsa ta bude
Yanzu dai akwai alamun da ke nuni da cewa Darya zata iya haifan yaron dake cikinta ‘dan bakwaini, wato wanda ba’a gama halittarsa ba, zata haifeshi nan da wata daya, wato watan August, kuma ance ba zata iya haihuwa da kanta ba
Yarinyar tayi fice a kafofin sada zumunta na Kasarsu, inda take da mabiya sama da rabin miliyon, kuma tana makarantar sakandare, ta bayyana cewa daukar ciki yana da wahala, yana haifar da matsaloli, tace hatta sauka daga kan gado yana bata wahala, kuma bata iya fita waje, abinci ma sai an kawo mata
Ina kungiyoyin kare hakkin yara kanana na duniya? Ina kungiyoyin gurbatattu ‘yan Boko aqeedah da manyan karuwai masu zaman kansu? to ga aiki ya sameku a Kasar Rasha, yaro yaci zarafin yarinya domin ba su kai shekaru 18 da kuke ikirari sai an kai ba
To wannan shine cikakken ma’anar da zinar wuri gwanda auren wuri
Allah Ka kare Musulunci daga sharrin masharranta Amin