Uncategorized
ZAN IYA YIWA BUDURWA SALLAMA ?
Advertisment
ZAN IYA YIWA BUDURWA SALLAMA ?
Tambaya:
DR barka da assubah, malam maye hukuncin yima mata sallama a lokacin da ake kiliya da su a kan hanya?, ‘yan mata da kuma na aure wanda na sani da wanda ban san su ba, sai bayan na musu sai kuma naji duk na tsargi kaina.
bissalam
bissalam
Amsa:
Wa alaikum assalam, An tambayi Imamu Malik game da yin sallama ga mata, sai ya ce: Game da budurwa bana son hakan, Amma game da tsohuwa,to Ba zan hana hakan ba, kamar yadda ya zo a Muwaddah.
Wannan shi ne mazhabar mafi yawan malamai.
Ya halatta ka yiwa maharramarka sallama ko matar da ka tabbatar ba za ku fitunu da juna ba.
Ya halatta ga namiji ya yiwa taron mata sallama, lokacin da suke da yawa,saboda hadisin Abu-dawud: Annabi (S.a.w) wuce taron wasu mata sai ya yi musu sallama.
Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Zarewa. 20/9/2016
Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Zarewa. 20/9/2016
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com