Kannywood

A Karon Farko Rahama Sadau Na Shan Yabo Bayan Ta Wallafa Hotonta Cikin Shigar Kamala

Advertisment

A Karon farko fitattaciyar jaruma a masana’antar shirya fina-fina ta Kannywood, Rahama Sadau ta yi shigar kamala wacce wasu ke ganin ita ce shigar da cikakken ɗan Musulmi Bahaushe ya kamata yayi.
Jaruma Rahama Sadau ta saka hoton nata ne a shafinta na kafar sada zumunta na Facebook inda ta samu mabiyanta sama da mutane dubu 3.9 suka yaba a cikin ƙanƙanin lokaci.
Idan har zaku iya tunawa dai Rahama Sadau na karɓar surutu kala-kala daga wajen al’umma musamman ma idan tayi wata shigar dake nuna surar jikinta.
Ko a ƴan kwanaki ma sai da jarumar ta haifar da ce-ce-ku-ce a shafukan sadarwa kan irin shigar da ta yi.
Dayawa daga cikin mabiyanta dai sun yi fatan cewa, jarumar za ta ci gaba da sanya suturar da bata saɓa da al’adun Bahaushe ba.
-Idon Mikiya

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button