An sanya Ranar Daurin Auren Afakallahi Da Rukayya Dawayya
Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Isma’il Na-Abba Afakallahu, zai Angwance tare da Tsohuwar Jarumar Finafinan Hausa Rukayya Dawayya.


Za a daura auren ne, a ranar 4 ga watan Nuwamba 2022, da misalin karfe 2pm na rana, a Masallacin Juma’a na Tishama da ke garin Kano.
Kamar yadda Shugaban tace fina finai na kannywood Ismail Na Abba Afakallahu ya bayyana a shafinsa na sada zumuta…
“Alhamdulilah muna gyatar yan uwa da Abokan Arziki idan ba’a samu dama ba ayi mana Addu’a”
Wanda na take itama amarya ta sake wallafa wanann katin gayyatar yan uwa da abokan arziki zuwa wajen daurin aurensu da za’a yi sati mai zuwa da yarda Allah.
Nan take jaruman kannywood maza da mata sunka fata yimusu fatan Alkhairi tare da sake wallafa wannan katin gayyata domin sanarda sauran al’umma.
A madadin shafin hausaloaded da mabiyanta muna yiwa amarya da ango fatan Alkhairi Allah ya nuna mana wannan rana amen.