Kannywood

Ban taba sauya Jam’iyya ba tun da na fara siyasa – Sani Danja

Advertisment

Hoto Daga Instagram : Sanidanja

Fitaccen Jarumi kuma mawaki a masana’antar shirya fina-finan hausa ta Kannaywood, Sani Musa Danja ya ce, ya tsaya waje guda a Jam’iyyar PDP, ba ya bin wasu ‘yan siyasa, kamar yadda wasu ‘yan masana’antar fina-finan hausa ke yi.
Kamar yadda dalafm na ruwaito Sani Danja, ya bayyana hakan ne ta ciki wani shiri na musamman da ya gudana a gidan rediyon Dala a ranar Labara.
Ya na mai cewa, “Har shan ruwa wasu ‘yan siyasar sun taba gayyata ta, amma wannan bai ja hankali na na bar Jam’iyyar PDP ba har yanzu ina cikin ta”.
Ya kuma ce, “Har rufe min shago an yi, an kuma hana mu yin sana’ar Film a Kano, amma hakan bai sa mun sauya Jam’iyya ba mu na nan a inda aka san mu”. Inji Sani Danja
Sani Danja ya kuma kara da cewa, nan gaba kadan za a ji matsayar su a siyasa, amma kawo wannan lokaci ya na nan a Jam’iyyar PDP har yanzu.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button