Labarai

Za’a Kafa Majalisar kasashen musulmi Duniya – Recep Tayyib Erdogan

Wani labari na gani wanda zai faranta zuciya da ran duk wani Musulmin duniya
Ance jinin sojojin Daular Usmaniyyah Sheikh Recep Tayyib Erdogan ya bayyana sunayen wasu daga cikin kasashen Musulmin duniya wadanda suka bashi goyon baya domin a kafa sabuwar majalissar dinkin duniya a karkashin Musulmi zalla
“Wata majiya mai karfi daga fadar shugaban Kasar Turkiyya tace shugaba Erdogan ya bayya wasu kasashen Musulmin duniya da suke goyon bayansa a yunkurin da yake yi na kafa sabuwar Majalisar dinkin duniya mai suna MUSLIM UNITED NATION (MUN)
Ga jerin kasashen da suka goyi bayan shirin kamar haka, kamar yadda shugaban na Turkiyya ya bayyana.

Recep Tayyib Erdogan

(1) Gwamnati Kasar PALASDIN Tace:
“Kafa sabuwar majalissar dinkin duniya wacce za ta kunshi kasashen Musulmi zalla, zai taimaka mana wajen samun ‘yancin kan kasar mu”
(2) Gwamnati Kasar IRAN tace:
“Shirin yana da kyau don zai kawo karshen zaluncin da Amurka ke yiwa kasashen Musulmi.”
(3) Gwmnati Kasar TUNISIA tace:
“Zamu bada duk wata gudunmawa don tabbatar da wannan kuduri.”
(4) Gwamnatin Kasar IRAQI tace:
“Yunkurin abu ne mai kyau kuma muna goyon baya.”
(6) Gwamnati Kasar OMAN tace:
“Idan hakan zai kawo hadin kan musulmin Duniya to muna maraba da shirin.”
(7) Gwamnatin Kasar QATAR tace:
“Muna fatana Allah ya tabbatar da wannan kuduri namu.”
(8) Gwamnatin Kasar JORDAN tace:
“Zamu taimaka da duk abinda ake bukata don cimma wannan kuduri.”
(9) Gwmnatin Kasar BAHRAIN tace:
“Kasar mu tana maraba da wannan mataki.”
(10) Gwmnatin Kasar ALGERIA tace:
“Muna fatan wannan majalissar kar ta zama kamar ta hadin kan kasashen larabawa wacce ba ta tabuka komai.”
Wallahi naji dadin wannan labari matuka sosai, kafa majalisar kasashen Musulmi zai kawo karshen wariya da banbancin da ake nunawa Musulmi a duniya, domin majalisar dinkin duniya UNITED NATION (UN) majalisa ce kawai ta shan shayi da aka kafata da manufar danne hakkin Musulmi
Muna fatan Allah Ya tabbatar da wannan kuduri na shugaba Recep Tayyib Erdogan Amin
Mun dauko wannan labari daga shafin datti assalafy

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button