Labarai
Za Kuyi Matukar Nadama Idan Har Aka Sauke Pantami ~ Sheikh Ahmed Gumi Ga Yan Najeriya
Advertisment


Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya gargadi yan Najeriya akan batanci da kuma kiyayya da wasu suke wa Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Dijital, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami.
Shehun malamin ya yi wannan gargadi ne a daidai lokacin da wasu ke kiran shugaban kasa akan ya kori ministan saboda abunda suka kira da cewar yana ta’ammuli da kungiyoyin yan ta’adda, kamar yadda shafin Madubi-H ya jiyo.
Wanda duk wannan abubuwan da yake fitowa ya danganta Pantami da ta’adddanci tunda yace dole sai an hada NIN da layin waya wanda kunsan cewa akwai marar gaskiya sosai masu aiki da layukan waya.





