Masu zanga-zanga sun sace rigar-mama da kamfai na Firaministar Bangladesh mai murabus
Dubban masu zanga-zanga a Bangladesh sun wawashewa tare da lalata gidan tsohuwar Firainista Sheikh Hasina a birnin Dhaka.
Wannan ya biyo bayan murabus din Hasina a matsayin PM a jiya Litinin, bayan da aka shafe makonni ana zanga-zangar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane mafi tsanani tun bayan kafar Kudancin Asiya fiye da shekaru hamsin da suka gabata.
A cewar BBC, Hasina ta nufi Tripura, babban birnin Agartala a Indiya, bayan ta yi murabus.
Hasina, mai shekaru 76, da ‘yar uwarta sun dauki jirgin sama mai saukar ungulu na soji zuwa jihar Bengal ta Gabashin Indiya, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.
An ce an tilastawa Firaministar yin murabus ne bayan wata gagarumar zanga-zangar nuna adawa da gwamnatinta kan tsarin raba kaso 30 bisa 100 na ayyukan gwamnati ga dangin tsoffin sojoji da suka yi yakin ‘yancin kai a Bangladesh a shekarar 1971.
Hotunan bidiyo sun dauki lamarin hargitsi yayin da masu zanga-zangar suka yi baje kolin kan tituna dauke da kayansu daga gidan Hasina.
Kayayyakin da aka wawashe sun hada da kamfai, rigar mama, kayan dafa abinci, kayan daki, dabbobi, da na’urorin lantarki.
Wani hoto ya nuna wani mutum sanye da kayan mata kuma yana dauke da bokitin roba cike da kaya, yayin da wani kuma ya nuna wani matashi rike da riga mai launin shudi.