Labarai
Fantami,Yafi Kowanne Minista Kokari Amma yan yahoo yahoo sun sakoshi a gaba – cewar sheikh Jingir
Shugaban majalisar malamai na kasa na Kungiyar Izala, Sheikh muhammad sani Yahaya Jingir, yace Gabadaya ministocin Gwawbnatin buhari, babu wanda yakai Dakta Isah Ali pantami Aiki, da kawo cigaba a ma’aikatar sa . Amma wasu bata gari marasa kishin nijeriya suke so a cireshi.
Sheikh Jingir, yace babu wanda suka saka pantami, a gaba Kamar yan yahoo saboda ya hanasu zambar jama’a da satar kudaden Al’umma wanan yasa suke so su kullawa pantami sharri amma bazasuyi nasara ba.
Sheikh Jingir, yana wanan jawabi ne a jiya yayin da yake gabatar da nasihar juma’a a babban massalacin juma’a na Yan taya dake birnin Jos.
Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano