Labarai

Tsintar gawar shugaban APC: Buhari ya yi martani tare da aike wa jami’an Tsaro sako Cin Fushi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce wajibi ne jami’an tsaro su yi iyakar kokarinsu wurin tabbatar da sun dakatar da kashe-kashen da ya ta’azzara a Najeriya.
Shugaban kasan ya fadi hakan ne bayan samun labarin kisan Philip Shekwo, shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa, jaridar The Cable ta wallafa yayin da mu kuma mun dauko daha da legit
Sai da aka sace Shekwo a gidansa da ke Lafia, ranar Asabar da daddare, daga baya aka tsinci gawarsa.
A wata takarda ta ranar Lahadi, wacce Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya saki, ya yanki inda shugaban kasa yake fadin kokarin mamacin wurin bunkasa jam’iyyar, wanda ba za a taba mantawa da shi ba a tarihin APC din jihar Nasarawa.
Shugaba Buhari ya ce za a tabbatar an yi tsattsauran bincike don a gano ko aikowa aka yi don a kashe shi, ko kuma garkuwa da shi aka yi, tukunna aka kashe shi.
Ina matukar jin takaicin kisan Philip Shekwo. Mutum ne mai kirki da fara’a.
“Ya yi matukar kokari wurin bunkasa jam’iyyar APC a jihar Nasarawa, ba za a taba mantawa da shi ba. Muna masa fatan rahama,” cewar Buhari.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Emmanuel Bola Longe, wanda ya tabbatar da hakan a wata hirar wayar tafi da gidanka da yayi da jaridar Leadership, ya ce ‘yan bindiga masu tarin yawa ne suka tsinkayi gidan shugaban APC.
 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button