An kama ma’auratan da suka sayi jariri, har sun shirya bikin rada masa suna


Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta ceto wani jariri dan watanni biyu daga hannun wasu ma’aurata, Mista James da Uwam, a yayin bikin radin sunan yaron a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin,ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce ma’auratan sun biya Naira miliyan 2,350,000 don siyan jaririn daga hannun wani da ake zargin mai fataucin yara mai suna Loretta Nelson, wanda ya sayi jaririn a hannun wani Fasto mai suna Peter Udoh a kan N1. 450,000.
Hundeyin ya ce Udoh ya sayi jaririn ne a kan Naira 500,000 daga hannun wata mai suna Gloria Sunday da ake zargi da satar jaririn a ranar 11 ga watan Yulin 2024, lamarin da ya sa mahaifiyar jaririn ta kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.
Bayan rahoton, Hundeyin ya ce ‘yan sandan sun yi bincike, wanda ya kai su ga cafke wasu da ake zargi da aikata laifin da jami’an ‘yan sanda da ke sashin Oko Oba suka kama.
Ya ce, Jami’an ‘yan sanda sun dauki matakin kama Gloria Sunday wadda a lokacin da ake yi mata tambayoyi ta ce ta sayar da jaririn a kan N500,000 ga wani Fasto Peter Udoh.
Fasto Udoh, wanda daga baya aka kama shi a garin Ikene, jihar Ogun, ya amince ya sayar da jaririn kan kudi N1,450,000 ga wata Loretta Nelson da aka kama a Festac Town, Legas.
Hundeyin ya ce, Nelson ya amsa cewa ya sayar da jaririn ne a kan Naira 2,350,000 ga wani Mista da Mrs. James Uwam da aka kama yayin bikin nadin yaron da aka sace.