Da Duminsa: Dangote ya maka matarnan da ta nuna hotunansa suna soyayya, inda ya zargeta da nunawa Duniya tsiraicinsa
Matarnan ta kasar Amurka da ta bayyana hotunan soyayyar ta da Attajirin Africa, Aliko Dangote zata fuskanci shari’a bayanda Dangoten ya makata a kotu.
Rahotanni daga PMNEWS sun bayyana cewa Dangote ya maka matar a wata kotin Miami dake Florida a kasar Amurka inda ya nemi diyyar dala 30,000 saboda zargin bata suna.
Rahoton Yace Dangote ya zargi matar ta wallafa hotunan tsiraicinsa ba tare da izininsa ba. A hotunan da matar, Autum Spikes ta wallafa, an ga mazaunan Dangote sun bayyana.
shafin Hutudole na ruwaito.Saidai daga baya ta gogesu kuma ta karyata cewa ta yi amfani da hakanne wajan neman suna. Saidai ta gargadi Dangoten da cewa wannan kara da ya shigar zata sa wasu karin sirrikanshi da ba’a sani ba su fito fili yayin sauraren shari’ar.
Ta kuma bayyana cewa Dangoten yayi yunkurin bata kudi dan kada ta yi magana akan soyayyar da suka yi amma ta kiya.
Majiyar tace, amma Har yanzu shi Dangote ya, ya ki cewa komai game da lamarin.